Jaruma Mai Kayan Mata: Sai An Biya N1m Ake Gani Na Ido-Da-Ido, Magana Ta Waya Kuma N250,000

Shahararriyar mai bada magungunan mata da sha'awa, Hauwa Muhammad da aka fi sani da Jaruma, ta bayyana cewa tana karbar N1m don ganinta ko N250,000 don magana da ita a waya. Ta bayyana hakan ne ga uwar dakinta, OJ Posharella, yayin shirin 'Real Housewives of Abuja' kashi na biyu da ake nuna wa a Showmax,

  • Hauwa Muhammad, shahararriyar mai sayar da kayan mata ta bayyana cewa sai an biya Naira miliyan 1 ake ganin ta ido da ido don neman shawarwari ko magani
  • Jaruma ta kuma ce idan ana son yin tuntubarta ta wayar tarho shi kuma sai an biya N250,000, ta kara da a kan biya ta don zuwa taro ko wani wurin haduwar mutane
  • Fitacciyar mai maganin matan ta kuma yi alfaharin cewa babu wata ko wani mai maganin mata da ya fita samun albashi mai tsoka a cikin shekara 10 da suka shude a kasar

Shahararriyar mai bada magungunan mata da sha'awa, Hauwa Muhammad da aka fi sani da Jaruma, ta bayyana cewa tana karbar N1m don ganinta ko N250,000 don magana da ita a waya.

Ta bayyana hakan ne ga uwar dakinta, OJ Posharella, yayin shirin 'Real Housewives of Abuja' kashi na biyu da ake nuna wa a Showmax, rahoton Premium Times.

Kara karanta wannan

Kaico: An debi 'yan kallo yayin da saurayi ya kama budurwa a otal tana karuwanci

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ta yi nuni da cewa matan sun yi sa'a sosai na ganinta araha tana zaune tare da su domin ba ta cika halartar taro ba kuma ana biyanta kafin ta zo.

A ganni ido-da-ido sai an biya Naira miliyan 1, waya kuma N250,000 - Jaruma

Jaruma, wacce ke alfahari da kanta a matsayin mai maganin mata mafi aminci, mafi nasara kuma wacce aka fi biya albashi a shekaru goma da suka shude ta ce:

"Eh, dama ce. Nawa ne? Yin magana da jaruma a waya N250,000 ne. Ganin ta ido da ido kuma Naira miliyan 1. Su wanene wadannan 'talakawan'?"

Wannan zancen ya haifar da hatsaniya tsakanin mai maganin matan da Gimbiya Jecoco a casun saka kananan kaya da Tutupie ta shirya a shiri na uku.

Daga bisani, hakan ya sa Jaruma ta tashi ta bar wurin casun, ta bar hadimarta ta gana da wadanda suka taho ganinta don neman magani ko shawarwari na harkokin daka.

Kara karanta wannan

Bayan Shekaru 8, Matashiya Ta Haifi Yara Biyar, Maza 3 Da Mata 2, Bidiyon Ya Yadu

Jaruma Ta Yi Magana Bayan Kotu Ta Ce A Sake Kamo Ta

A baya kun ji cewa fitacciyar mai maganin mata a Najeriya, Hauwa Muhammad aka Jaruma ta magantu kan dalilin da yasa ba ta tafi babban kotun Zuba da ke Abuja ba don cigaba da shari'a.

Tunda farko, jami'an tsaro sun kama Jaruma kan zargin yada karerayi kan hamshakin attajiri Ned Nwoko, mijin jarumar Nollywood Regina Daniel.

A wani rubutu da ta wallafa a shafinta na Instagram ta bayyana cewa ta tashi ba ta da lafiya ne hakan yasa ba ta samu ikon zuwa kotun ba amma za ta tafi.

Asali: Legit.ng

ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHC6yKyfmpyZZH52fpdtaHBlkpavo63NZqSan5Gjrm66kKZknaeeYrSius2iZKeZXZ6xsHnDmmSinJ9iu3OBj2lnaWWbqrqiecOopWalkZyur62MrZhmr5Gurm62wKuspplf

 Share!